Kakaitaccen Tarihin Mawaki NURA M INUWA

NURA M INUWA


 Taccen Tarihin Mawaki Nura M Inuwa
Tattaunawa Kai Tsaye Tafeda Jarumi Abas
Sadiq Cikin Shirin Gani Da Idonka.
ABBAS SADIQ : Da farko dai masu Sauraro
zasuso suji takai taccen tarihinka?
Nura M Inuwa : Da farko dai sunana Nura Musa
Inuwa wanda a yanzu akafi sani da Nura M
Inuwa, Ni Haifaffen Garin Kano ne Gommaja
Karamar Hukumar Dala.
Nayi Makaranta na na primary school a masaka
special primary school daganan na wuce
Gommaja two inda inda acan nayi secondry
school dina daga nan kuma cikin ikon ubangiji
banci gaba ba, Daganan sai na fara harkar
waka.
ABBAS SADIQ : Nura M Inuwa me yaja hankalin
kane har ka fara harkar Waka?
Nura M Inuwa : Aah! Alhamdulillahi Nidai tun
farko bani da wani dalili da yaja hankalina na
fara harkar waka, sabo da ya samo asaline tun
ina yaro ni kaina haka kawai inayin waka haka
kuma idan akan batamun raj nakanyi waka
domin in huce bacin ran nan da akamun hakama
idan an faranta mun nakanyi waka.
Ta yadda tun bansan kalar ko launin wakaba da
yadda take nidai kawai inayi, daga baya kuma
saina sawa raina cewa inason in fara waka, ina
girma ina girma sai nazo na fara Makaranta,
Sabo da haka Allah cikin ikon sa sai na fara
waka a Makaranta inda nakanyi waka ta Yabo
musamman in ana Maulidi inzo in rera a haka a
haka abu yanaci gaba.


Kancewar ba wakar Yabon na fara yiba, Sai
akazo idan na kalli Film "Misali" Ace wannan
Film din na daya ne lokacin ana yin film pert 1
and 2 to a lokacin sai ya zamana ina iya kirkirar
waka ta kaina idan na kalli film na daya kuma
ya burgeni to sai in kirkiri waka tawa ta kaina
wacce nake ganin itace zata zama ci gaban
wannan shirin film din.
Da haka da haka inayi Allah cikin ikonsa har
nazo na fara Waka dana farane kuma sai na
fahimci cewa zan iya daukar waka a mastayin
haryace ta tura sakon ni na fadakarwa sannan
kuma zan iya rikanta a matsayin sana'a kamar
yadda take yanzu a wurina.
Wannan Shine Kadan Daga Cikin Abunda Muka
Dan Tsakuro Muku Dangane Da Tarihin Mawaki
Nura M Inuwa, Akwai Yiwuwar Ci Gaba Da
Kawo Muku Wannan Tattaunawa Nan Bada
Jimawa Ba.

Comments

Popular posts from this blog

Ramadan: Month of Ibadat and Repentance

YADDA ZAKA SACE ZUCIYAR YARINYA DA SAURI

Why we need better husbands in our societies.