Izala Ta Fara Aiwatar Da Shirinta Na tallafawa Marayu Da Gajiyayyu A Wurren Tafsirai





 Ibrahim Baba Suleiman
Duk wanda yake bibiyar irin cigaban da wannan
kungiyar takeyi tun lokacin da shugabanta na
farko ya rasu Alhaji musa maigandu Allah ya
masa Rahman, zaiga cewa lallai al'ummar
musulmin najeriya sun shaida irin cigaban da
wannan kungiyar ta samu musamman ta
bangaran tallafawa marayu da gajiyayyu da
zawarawa Wanda Sheikh Bala Lau Ya assasa a
kasancewar Sa Shugaban Izala.

Shugaba sheikh Bala Lau ya bada umarni ga
dukkan malaman kungiyar da shugabanni akan
kafa kwamitocin tallafawa marayu a dukkan
matakan shugabanci na kungiyar tun daga kasa
har zuwa kananan hukumomi. bugu da Kari an
umarci dukkan malaman kungiyar da aka tura
tafsirin Ramadan dasu tabbatar sun kaddamar
da neman tallafawa marayu A wuraren Da suke
gabatar Da Tafsirai, Wannan shekara ba itace ta
farko ba.

Yanzu abun farin ciki tuni wasu majalisin tafsirai
suka fara farantawa marayun ransu kamar jahar
kano wurin tafsirin Dr. Abdullah saleh Pakistan
da jahar kaduna wurin tafsirin sheikh kabiru
Gombe da jahar Katsina wurin tafsirin sheikh
yakubu musa, Da Jihar Gombe wajen Tafsirin
Sheikh usman Isah Taliyawa Da Dai sauran
wurare a fadin kasa
Dr Abdullahi saleh pakistan
Allah ya tsawaita rayuwar wannan jagora cikin
tallafawa addininsa, Ya karbi ayyukan Da ake yi
kullum.

Comments

Popular posts from this blog

Ramadan: Month of Ibadat and Repentance

YADDA ZAKA SACE ZUCIYAR YARINYA DA SAURI

Why we need better husbands in our societies.